Tun daga tsakiyar wannan wata da muke ciki, Sin da Amurka su ke cudanya a bangarori daban-daban. Game da hakan, Sin ta bayyana cewa, kasashen biyu za su samu nagartattun ci gaba masu armashi tare da samar da alfanu ga al’ummun duniya, a mabambantan bangarori, illa dai suka yi hadin gwiwa.
Manazarta na ganin cewa, ana fitar da sako mai yakini, duba da cewa bangarorin Sin da Amurka suna kara mu’ammala tsakaninsu, a daidai wannan lokacin da ake sauya gwamnati a kasar Amurka.
- Yadda Sin Da Kasashen Afirka Ke Hadin Gwiwar Zamanantar Da Ayyukan Noma
- Kasar Sin Ta Bukaci EU Ta Samar Da Ci Gaba Game Tattaunawar Da Suke Yi Kan Farashin Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Sin
A wata mai zuwa, Amurka za ta samu sabuwar gwamnati, kuma zababben shugaban kasar Donald Trump ya bayyana a kwanan baya cewa, za a iya warware kowacce matsala da ake fuskanta a duniya, idan Sin da Amurka suka hada kansu. Daga furucin nasa, za a iya fahimtar cewa, Amurka ta fahimci muhimmancin hadin kanta da kasar Sin, wanda mataki ne da zai amfana wajen rage rashin tabbaci a nan gaba, musamman ma a fannin huldar kasashen biyu. Hakika hanyar da ta fi dacewa, wadda sabuwar gwamnatin Amurka za ta iya bi, ita ce mutunta tsare-tsare da hanyoyin hadin gwiwa da bangarorin biyu suka riga suka tsara, da ma gabatar da karin sabbin hanyoyi da dabaru masu alaka da yunkurin kyautata huldarsu ta hadin kai.
Duk duniya sun kai ga matsaya daya cewa, kyautatuwar huldar Sin da Amurka mai dorewa ba al’ummar kasashen biyu kadai ta shafa ba, har ma da bayar da babbar ma’ana ga makomar Bil Adama ta bai daya. Duniya na fatan ganin bangarorin biyu za su kara tuntubar juna, da habaka hadin gwiwarsu, da warware matsaloli bisa iyakacin kokari a tsakaninsu, ta yadda za a sauke nauyin dake wuyan wadannan manyan kasashe guda 2, don karfafa hadin gwiwarsu da zai amfanawa al’ummar duniya, gami da samar da karin tabbaci da al’ummun kasa da kasa suke bukata. (Amina Xu)