A yau Jumma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na Angola Joao Lourenco a nan birnin Beijing, inda shugabannin biyu suka sanar da daga matsayin dangantakarsu zuwa ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare.
Xi Jinping ya bayyana cewa, Sin abokiyar dogaro ce kuma sahihiyar abokiyar hulda ga kasashen Afrika wajen kare cikakken ‘yancinsu da inganta ci gabansu da farfadowarsu. Ya ce, Sin na goyon bayan kasashen Afrika da ma Tarayyar Afrika (AU), a kokarinsu na warware batutuwan da suka shafi Afrika bisa dabarun Afrika da kuma kare tsaro da zaman lafiya a nahiyar.
- Tallafin Da Amurka Ta Baiwa Gaza Wasan Kwaikwayo Ne
- Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoto Mai Taken “’Yancin Fadin Albarkacin Baki A Amurka: Gaskiya Da Hujjoji”
Ya kara da cewa, a shirye Sin take ta karfafa cudanya da Angola da sauran kasashen Afrika, domin kare muradun bai daya na kasashe masu tasowa da hada hannu wajen tabbatar da adalci da raba iko tsakanin kasa da kasa da tabbatar da dunkulewar tattalin arzikin duniya domin kowa ya amfana da kuma inganta gina al’umma mai makoma ta bai daya ga dukkan bil Adama.
A nasa bangare, Joao Lourenco ya ce, Sin ce kasa ta farko da ta samar da taimako mai muhimmanci ga Angola a lokacin da yakin basasar kasar ya kawo karshe da kuma yayin fama da annobar COVID-19, yana mai cewa, Angola na bayyana matukar godiyarta. Ya ce taimakon kasar Sin da hadin gwiwa da ita, sun inganta ginin ababen more rayuwa a Angola da habaka tattalin arziki da kyautata zamantakewar al’umma, lamarin da ya zama kyakkyawan misali na dangantakar moriyar juna. Ya ce kasar Angola na maraba da kamfanonin kasar Sin su zuba jari a kasar domin taimakawa ci gaban kasar da ma farfadowarta.
A wannan rana kuma, firaministan kasar Sin Li Qiang da shugaban kwamitin kula da harkokin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji sun gana da shugaban Angola bi da bi. (Fa’iza Mustapha)