Kwanan baya, Isra’ila ta ci gaba da kaiwa zirin Gaza hare-hare, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka da dama. Amurka ce ta samar da da yawa daga cikin makaman da Isra’ila ta yi amfani da su. Bisa labarin da shafin yanar gizo na jaridar kasar Isra’ila wato Ha’aretz ya bayar, an ce, Amurka ta shafe tsawon watanni 5 tana jigilar makamai ta sama zuwa Isra’ila.
A wani bangare Amurka na tallafawa Isra’ila da makamai, yayin da a wani bangare na daban kuwa, ta yanke shawarar jefa wa fararen hula a Gaza abinci daga sama. Sai dai daga cikin dubban abincin da ta jefa, yawancinsu sun fada ne cikin teku, wadanda suka kasa biyan bukatun fararen hular Gaza da yawansu ya haura miliyan 2. Ban da wannan kuma, sakamakon yadda laimar sauka daga jirgin sama masu dauke da abincin sun gaza budewa cikin lokaci, ya sa abincin ya fada kai tsaye kan wasu gidaje da mutane dake kasa, abin da ya sa mutane 5 suka mutu.
- Mun Gano Famfo 5,570 Da Ake Amfani Da Su Wajen Satar Danyen Mai — NNPCL
- Jamhuriyar Congo Tana Son Karfafa Zumunta Da Hadin Gwiwa Da Sin
Shin ko da gaske ne Amurka tana mai da hankali kan rikicin jin kai dake faruwa a Gaza?
Kungiyoyin jin kai da dama sun yi tir da hanyar da Amurka ta zaba ta samar da tallafin jin kai ta hanyar jefa abinci daga sama. A ganinsu, a maimakon bukatar kawarta wato Isra’ila da ta bude hanyoyin jin kai, ko daina samarwa Isra’ila makamai, Amurka ta zabi hanyar da ba ta dace ba, wato jefa abinci daga sama, kuma burin da take neman cimmawa shi ne samun goyon baya daga masu kada kuri’u a gida.
Ban da wannan kuma, shugaban kasar Amurka Joseph Biden ya sanar da shirin kafa wata tashar jirgin ruwa ta wucin gadi a gabar tekun bahar Rum dake Gaza, don baiwa yankin tallafin jin kai. Hakan ya jawo suka daga masu bibbiyar kafar sada zumunta ta X, wadanda suka yi zargin cewa, Amurka tana da karfin dakatar da rikicin da ake fuskanta a Gaza muddin ta daina samarwa Isra’ila makamai, amma ta yi wasan kwaikwayo na samar da tallafin jin kai.
Tallafin da Amurka ta bayar da kyar sun isa hannun fararen hula, amma makaman da ta samar sun halaka mutane masu dimbin yawa. ‘Yan siyasar Amurka su kan yi wasan kwaikwayo don samun kuri’u, amma a wannan karo masu gudun hijira ke yin asara, wadanda ba su da abinci ba su da gidaje kuma ba su da tsaro, ballantana hakkin Bil Adama. Shin ko ‘yan siyasar Amurka ba su jin kunya? (Mai zana da rubutu: MINA)