Mamba a ofishin hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana dakarta a ofishin hukumar lura da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar Wang Yi, da mashawarcin shugaban kasar Faransa kan harkokin diflomasiyya Emmanuel Bonne, sun jagoranci taron tattaunawa bisa matsayin koli na kasashen biyu karo na 26.
Yayin tattaunawar ta jiya Asabar a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, Wang Yi, ya ce shugabannin kasashen Sin da Faransa na ci gaba da wanzar da cudanya a ‘yan shekarun baya bayan nan, sun kuma samar da wata alkiblar ci gaban dangantakar Sin da Faransa, da Sin da Turai.
- Yadda Ake Hadin Ɗan Waken Zamani
- ASUU Ta Fara Gangamin Shiga Yajin Aiki Yayin Da Gwamnatin Tarayya Ta Kasa Cika Alkawari
Ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Faransa, wajen tabbatar da dangantakarta da Faransa ta ingiza ci gaban alakar Sin da Turai, da yaukaka yanayin zaman lafiya da daidaito a duniya baki daya.
Daga nan sai mista Wang ya gabatar da shawarwari guda 4, da suka hada da mayar da kudurorin da shugabannin kasashen 2 suka cimma matsaya a kai a matsayin alkibla, da kuma samar da karin ajandodin kyautata dangantakar sassan 2. Sai kuma ingiza hadin gwiwa, ta yadda za a yi amfani da fifikon gargajiya na sassan 2, da lalubo sabbin damammaki don ingiza hadin gwiwa bisa sabon karfi na samar da ci gaba. Na uku kuma, sassan biyu su dage wajen cin gajiya daga bikin shekarar raya al’adu da yawon bude ido na Sin da Faransa, da ingiza musayar al’ummu tsakaninsu. Kana na karshe, su hada hannu wajen goyon bayan wanzuwar cudanyar sassa daban daban.
A nasa tsokaci kuwa, mista Bonne, cewa ya yi Faransa na dora muhimmancin gaske ga kawancen gargajiya, da amincewa juna tsakaninta da Sin, za kuma ta nacewa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da ci gaba da raya musaya ta kut da kut tsakanin manyan jami’ai tare da bangaren Sin, da tabbatar da cimma nasarar tsare-tsaren tattaunawa tsakaninsu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp