ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, June 21, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala

by Abubakar Sulaiman
2 years ago
Fitowa

Yayin da wasu ke daukar harkar fim a matsayin wata hanya na neman kudi kawai, daya daga cikin manyan dattijai a cikin masana’antar Kannywood Alhaji Dan Asabe Garba ko kuma Olala ya ce akwai wasu ayyuka da ba zai iya yi ba ko nawa kuwa za a ba shi.

A lokacin da zan shiga harkar fim, masoya,iyalai da ‘yan uwa sun so su hana ni saboda a nasu tunanin zan iya yin wani abinda zai iya zubar masu da mutuncinsu amma ganin ina matukar sha’awar harkar ya sa dole suka hakura na shiga amma da sharudda biyu, na farko shi ne ba zan taba fitowa a cikin shirin fim a matsayin Dan Daudu ba hakazalika ba zan fito a matsayin Kwarto ba.

  • Na Samu Wata Harkar Da Ta Fi Sana’ar Fim Kawo Kudade -Ali Dawayya
  • Ana Yi Wa ‘Yan Fim Kallon Malamai A Zamanin Baya -Ali Rabi’u Ali

Yanzu haka a kan wannan matsaya ya sa suka barni ina yin wannan harkar, saboda haka ko nawa wani zai bani a kan in karya wannan alkawari da na daukar wa ‘yan uwana da iyalina ba zan karba ba saboda mutunci ya fi komai in ji Dan Asabe Olala wanda ya shafe tsawon shekaru ana damawa da shi a masana’antar Kannywood.

ADVERTISEMENT

Dangane da kalubalen da masana’antar Kannywood ke fuskanta a halin yanzu, Olala ya ce daga cikin kalubale da ke damun Kannywood akwai rashin jari wanda ya sa an samu karancin yin fina-finai ba kamar a kwanakin  baya da za kaga ayyuka sun yi yawa ba,a wancan lokacin a kan hada karfi mutum biyu ko uku su shirya fim daya saboda za a kai fim kasuwa a sayar kowa a bashi kudinsa.

Amma yanzu saboda yadda aka koma fina-finai masu dogon zango da dama mutane basu da isassun kudaden da za su saka wajen shirya manyan fina-finai da ake shiryawa a yanzu, saboda haka da ace zan samu shugabancin wannan masana’antar zan mayar da hankalina kacokan wajen hada kan mambobin masana’antar ta Kannywood.

LABARAI MASU NASABA

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Sannan kuma in tafi wajen samo masu hannu da shuni domin su zo su zuba hannayen jarinsu a wannan masana’antar, zaka ga da dama mutane na sha’war zuba hannayen jarinsu a wannan masana’antar amma ba su san yadda za su yi ba ko kuma hanyoyin da za su bi wajen ganin ba su yi asarar kudadensu da su ka zuba a harkar ba.

Daga karshe Alhaji Dan Asabe ya shawarci matasa mata da maza da ke da sha’awar shigowa wannan masana’antar domin su fara harkar fim a kan duk wanda zai shigo ya tabbatar da cewar zai iya hakuri har zuwa lokacin da Allah zai nufi ya samu daukaka, domin kuwa a dare daya ba zai samu abin da yake so ba dole sai ya jajirce ya kuma yi hakuri kamar yadda wadanda yake gani sun samu daukaka suka yi kafin shima ya zama wani abu a Kannywood.

Fitowa
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi
  • Abubakar Sulaiman
    Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni
  • Abubakar Sulaiman
    Ƴansanda Sun Kama Mutane 5 Kan Satar Wayoyin Lantarki A Katsina
  • Abubakar Sulaiman
    Farashin Mai Na Iya Sauka Har Zuwa Dala $60 Kan Kowanne Ganga

MASU ALAKA

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina
Nishadi

Zan Iya Auren Namiji Komai Talaucinsa Muddin Muna Son Junanmu -Maryam Labarina

June 14, 2026
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
Nishadi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

June 14, 2026
Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro
Nishadi

Ban Taɓa Fitowa A Fim Na Yi Da-na-sani Ba —Habibu Yaro

May 31, 2026
Next Post
Yadda Wasan Manchester Derby Ya Kaya A Etihad 

Yadda Wasan Manchester Derby Ya Kaya A Etihad 

LABARAI MASU NASABA

An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 21, 2026
Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

June 21, 2026
Wasu Abubuwa Da Ke Sa Maza Hana Mata Fita Unguwa (Uwargida)

Nasiha Ga Uwargida Kan Zafin Kishi (1)

June 21, 2026
Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam

Kasar Sin Ta Karbi Bakuncin Taron Daidaita Batun Kare Hakkin Dan Adam

June 21, 2026
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi A Taron Majalissar UNHRC

June 21, 2026
Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

Ƴan Ta’adda Sun Ƙone Shingen Bincike Na NSCDC, Sun Sace Wani Mutum A Kebbi

June 21, 2026
Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada

Ɗanwasa Thomas Partey Ya Yi Rashin Nasara A Kotun Canada

June 21, 2026
Mutumin Da Ya Yi Matukar Tasiri Kan Shugaba Xi Jinping

Mutumin Da Ya Yi Matukar Tasiri Kan Shugaba Xi Jinping

June 21, 2026
Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni

Rikicin ADC: Ibrahim Little Ya Ƙaryata Zargin Ƙaƙabawa Jam’iyyar Shugabanni

June 21, 2026
Mutumin Da Ya Yi Matukar Tasiri Kan Shugaba Xi Jinping

Mutumin Da Ya Yi Matukar Tasiri Kan Shugaba Xi Jinping

June 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.