Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau Juma’a cewa, Sin na fatan kara hadin gwiwa da Ghana, don gaggauta bunkasuwar huldarsu ta abota bisa manyan tsare-tsare.
Yayin da Mao Ning take tsokaci game da cika shekaru 65 da kulla huldar diplomasiyya tsakaninsu, ta ce a ranar 5 ga watan nan da muke ciki, za a cika shekaru 65 da kalluwar huldar tsakanin kasashen biyu. Ta ce, Ghana na daya daga cikin kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara da suka riga sauran kasashe kulla huldar diplomasiyya da jamhuriyar jama’ar Sin, kuma ita ce kasa ta farko a wannan yanki da tsoffin shugabannin Sin suka ziyarta. Ta ce a shekarar bara, bangarorin biyu sun tabbatar da kafa huldar abota bisa manyan tsare-tsare a tsakaninsu, kuma Sin tana fatan kara hadin gwiwa da Ghana don amfani da wannan zarafi mai kyau wajen zurfafa dankon zumunci dake tsakaninsu, ta yadda al’ummun kasashen biyu za su ci gajiya. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp