A jiya Litinin ne kasashen Sin da Honduras suka fitar da sanarwar matsayar kasashen biyu bayan zantarwar shugabannin kasashen.
Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun amince cewa, huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Honduras bisa ka’idar kasar Sin daya tak, ta bude wani sabon babi a tarihin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, wanda ya dace da muhimman muradun kasashen biyu da jama’arsu.
Bangaren Honduras na ba da cikakken goyon baya da bin ka’idar kasar Sin daya tak, kuma tana adawa da “‘yancin Taiwan” ta ko wace fuska, da kuma duk wani mataki da ya saba wa ka’idar.
A karkashin tsarin hadin gwiwa na ziri daya da hanya daya, bangarorin biyu sun amince da karfafa hadin gwiwa da tsare-tsare na raya kasa, da zurfafa mu’amala da hadin gwiwa a fannoni daban daban, da aiwatar da ka’idojin tuntubar juna, da taimakawa juna, don cin moriyar juna.
Sannan gwamnatin kasar Sin ta sanya hannu kan takardar fahimtar juna, game da hadin gwiwar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya tare da gwamnatin kasar Honduras.
Hukumar bunkasa ci gaba da aiwatar da sauye-sauye ta kasar Sin ce ta bayyana hakan a Talatar nan, inda ta ce sassan biyu za su hada karfi da karfe wajen yin tafiya tare, da bunkasa nasarar manufofin sadarwa, da raya ababen more rayuwa, da fadada cinikayya, da hade fannonin hada-hadar kudade, da musaya tsakanin al’ummun sassan biyu.
Kaza lika a cewar hukumar, karkashin takardar fahimtar junan, za a karfafa hadin gwiwa a sassa daban daban, da bunkasa cimma moriyar juna, da koyi daga wayewar kan juna, da cimma nasarorin bunkasuwa da wadata.
Game da ziyarar shugabar Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento take yi a kasar Sin, da dimbin yarjejeniyiyin hadin gwida da aka kulla tsakanin Sin da Honduras, da sanyin safiyar yau Talata 13 ga wata, kafofin yada labaru na kasar Honduras sun ruwaito a shafunansu cewa, an bude sabon babin raya hulda a tsakanin kasarsu da kasar Sin, tare da ambato lamba “17” sau da dama, wadda ma’anarta ita ce takardun fahimtar juna guda 17 da kasashen 2 suka daddale, a fannin hada kai a sassa daban daban.
Kasar ta Honduras, muhimmiyar kasa ce a yankin Tsakiyar Amurka, kuma sabuwar abokiyar kasar Sin ce. A ranar 26 ga watan Maris na bana, kasashen Sin da Honduras sun kafa huldar jakadanci a tsakaninsu bisa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”.
Honduras ta zama ta 182, a jerin kasashen da suka kulla huldar jakadanci da kasar Sin.
A Jiya Litinin ne shugaba Xi Jinping na kasar Sin, da takwararsa ta Honduras Iris Xiomara Castro Sarmiento suka yi shawarwari, inda shugaba Xi ya jinjina wa yadda Castro ta tsai da kuduri mai matukar muhimmanci a tarihi, da kuma nuna aniyar siyasa.
A lokacin ziyarar shugaba Castro a kasar Sin, Honduras ta gabatar da rokon shiga bankin New Development Bank, kuma kasashen 2 sun amince da kaddamar da shawarwari kan yarjejeniyar ciniki cikin ‘yanci, sun kuma daddale takardar fahimtar juna kan hadin gwiwar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, tare da ba da sanarwar hadin gwiwar cimma ra’ayi daya.
Har ila yau, shugabannin kasashen 2 sun tsara shiri kan raya hulda a tsakanin kasashen 2, za kuma a kaddamar da hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki, da ciniki, da raya al’adu da dai sauransu, a kokarin samun ci gaba tare, ta yadda al’ummun kasashen 2 za su kara samun alherai.
‘Yan kasuwan Honduras suna da yakinin cewa, jatanlanle, da kankana, da kofi na Honduras, za su samu amincewa sosai a kasar Sin. Haka kuma, Honduras na maraba da kamfanonin Sin, da su zuba jari, da shiga ayyukan raya tattalin arzikin Honduras. (Mai fassarawa: Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan, Tasallah Yuan)