Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci bikin bude taron ministoci karo na 10 na dandalin tattauna hadin kan Sin da kasashen Larabawa a jiya Alhamis, inda ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kira taron koli karo na 2 tsakanin Sin da kasashen Larabawa a shekarar 2026, kuma tabbas, zai kasance sabon babin dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Larabawa. Haka kuma, ya bayyana ra’ayinsa game da yadda za a ci gaba da raya dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, yayin da ya gabatar da fannoni guda biyar da za su hada kai a nan gaba, domin gaggauta aikin kafa al’umma mai makomar bai daya a tsakanin Sin da kasashen Larabawa.
A bana, ake cika shekaru 20 da kafuwar dandalin tattauna hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Larabawa. Cikin shekaru 20 da suka gabata, bangarorin biyu sun raya dangantakar dake tsakaninsu inda ya zama abin koyi ta fuskar hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa. Yanzu, ana aiwatar da shirin “Ziri daya da hanya daya” a cikin kasashen Larabawa 22, lamarin da ya tallafawa al’ummomin bangarorin biyu kimanin biliyan 2.
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Tunisia Kais Saied
- Shugaban Kasar Sin Xi Jinping Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Tunisia Kais Saied
Kuma an lura cewa, a wannan karo, shugabannin kasashe 4 da suka hada da Bahrain, da Masar, da Tunisiya, da Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE, sun halarci bikin bude taron ministocin. Dangane da wannan lamari, Jaridar Arab Weekly ta fidda wani sharhi dake cewa, halartar shugabannin kasashen hudu taron, ya nuna jagorancin shugabannin Sin da kasashen Larabawa kan hadin gwiwar dake tsakaninsu, ya kuma nuna aniya da fatan shugabannin Sin da Kasashen Larabawa ta karfafa hadin gwiwarsu da kuma raya dangantakar dake tsakaninsu zuwa sabon matsayi. A yayin taron na wannan karo, an kuma gabatar da sanarwar hadin gwiwa ta Sin da kasashen Larabawa game da batun Falesdinu, inda aka yi kiran kawo karshen riciki a yankin Gaza, da kuma warware matsalar daga dukkanin fannoni, kuma bisa adalci.
Taron na wannan karo ya kasance sabon mafari ga kasar Sin da kasashen Larabawa, don haka ya kamata su dauki matakai masu dacewa yayin aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata, domin shimfida zaman lafiya da zaman karko ga duniyarmu dake cikin halin sauye-sauye. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)