Shugaban kasar Kenya William Ruto, ya gana da daraktan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Wang Yi a jiya Asabar, inda yayin zantawarsu, suka sha alwashin kara zurfafa hadin gwiwa karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya.
A kalaman sa, Shugaba Ruto ya jinjinawa kokarin kasar Sin, ta fuskar bunkasa alaka da Kenya, bisa ka’idar martaba juna. Ya ce Kenya za ta nacewa matsayin ta na zurfafa cikakkiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare tsakanin ta da Sin, kuma a shirye take ta karfafa musaya tsakanin jam’iyyun kasashen biyu. Kana za ta zurfafa hadin gwiwa da Sin a fannonin bunkasa layukan dogo, da samar da manyan hanyoyin mota, da tsumin ruwa, da sufurin jiragen sama, da makamashi da ake sabuntawa, karkashin hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya, da ma dandalin nan na hadin gwiwar Sin da Afirka na FOCAC, ta yadda za a kai ga ingiza dunkulewar yankunan Afirka, tare da cimma manyan sanarori tare.
Bugu da kari, shugaba Ruto, ya ce kasar sa na goyon baya, kuma ta shirya shiga a dama da ita a dukkanin tsare-tsaren samar da ci gaban duniya, wadanda kasar Sin ta gabatar.
A nasa bangare kuwa, Wang Yi cewa ya yi, kasar Sin na bin salon raya dangantaka da Kenya bisa manyan tsare-tsare, kuma Sin a shirye take ta yi aiki tare da Kenya, ta yadda za su yi amfani da damar cikar dangantakar su shekaru 60 da kafuwa, a matsayin sabon mafari na daidaita tsare-tsaren su na farfadowa, tare da mayar da hankali ga ci gaba da hadin gwiwa, da ingiza nasarar cikakken hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare dake tsakanin su, zuwa wani sabon matsayi a sabon zamani. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp