Jakadan kasar Sin a kasar Laberiya Yin Chengwu da ministar harkokin wajen kasar Laberiya Sara Nyanti, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha, a madadin gwamnatocin kasashensu, jiya Juma’a a Monrovia, babban birnin kasar Laberiya.
Minista Nyanti ta godewa gwamnatin kasar Sin bisa gagarumin goyon bayan da take bai wa kasar Laberiya, ta kuma ce yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tattalin arziki da fasaha da bangarorin biyu suka rattabawa hannu, za ta taimaka wa kasar Laberiya wajen cimma muradin raya kasa na ARREST. Ta ce Laberiya na son yin amfani da wannan dama wajen karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannonin raya kasa, da tattalin arziki, da cinikayya, gami da zuba jari.
A nasa bangare, Ambasada Yin Chengwu ya ce, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin tana kokarin aiwatar da alkawurran da aka dauka a gun taron kolin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da aka yi a birnin Beijing a shekarar 2024, da kuma gudanar da da manyan tsare-tsaren da shugabannin kasashen Sin da Laberiya suka tabbatar. Ya ce kasar Sin tana son aiwatar da yarjejeniyar tare da kasar Laberiya, da kuma sa kaimi ga bunkasuwar hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp