Labarin da dan jarida ya samu daga ma’aikatar tsaron jama’a ta kasar Sin a yau Lahadi ya nuna cewa, a kwanan baya kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun gudanar da taron ministoci karo na biyu don yaki da laifukan zambar da ake aikatawa ta hanyar sadarwar waya.
A gun taron, sassan da abin ya shafa na kasashen uku sun cimma matsaya kan zurfafa hadin gwiwar tabbatar da doka da oda, kuma za su ci gaba da yin hadin gwiwa wajen dakile laifukan zamba ta hanyar sadarwar waya a Myawaddy da sauran wurare, da kawar da harkokin zamba ta hanyar sadarwar waya gaba daya, da kame dukkan ma’aikatan da ke da alaka da laifin zamba, kana za su yi tsayin daka wajen yaki da dukkan laifuffukan da ke da alaka da zamba.
Bugu da kari, an fahimci cewa, tun daga farkon bana, sassan da abin ya shafa na kasashen Sin da Myanmar da Thailand sun yi hadin gwiwa wajen kaddamar da yaki da ayyukan zamba ta hanyoyin sadarwa a yankin Myawaddy, tare da kamewa da mayar da mutanen Sin sama da 5400 da ke da alaka da zamba zuwa Sin. Ana iya cewa, sun riga sun samu sakamako a bayyane. (Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp