Wakilin ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta Kasar Sin, kana darektan ofishin kula da harkokin waje na kwamitin tsakiyar, Wang Yi, da babban sakataren majalisar tsaro na kasar Rasha Sergei Shoigu, sun jagoranci taro na 20 na shawarwari kan manyan tsare-tsaren tsaro a tsakanin kasar Sin da kasar Rasha a birnin Moscow, fadar mulkin kasar Rasha. A yayin taron wanda aka yi jiya, bangarorin biyu sun yi tattaunawa mai zurfi kan manyan batutuwan dake shafar manyan tsare-tsaren tsaro bisa dukkan fannoni, inda suka cimma matsayi daya kan wasu sabbin batutuwa, tare da zurfafa fahimtar juna a tsakanin kasashen biyu.
Haka kuma, Sin da Rasha sun amince da aiwatar da ra’ayi daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma a fannin manyan tsare-tsaren tsaro, tare da inganta hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu kan manyan batutuwa.
Bugu da kari, bangarorin biyu sun cimma matsayi daya kan batutuwan dake shafar kasar Japan, tare da musayar ra’ayoyi kan ricikin Ukraine. Kana, sun gudanar da tattaunawa mai zurfi kan batutuwan dake shafar daidaiton manyan tsare-tsare na kasashen duniya, da dangantakar dake tsakanin manyan kasashe, da kuma yanayin yankin Asiya da Pasific da yankunan dake kewaye, da kuma sauran batutuwan dake jan hankulan kasashen biyu, domin daidaita matsayarsu kan manyan batutuwa masu ruwa da tsaki. (Mai Fassara: Maryam Yang)














