Ma’aikatar lafiya ta kasar Rwanda da ofishin jakadancin kasar Sin dake Kigali, sun rattaba hannu a kan wata yarjejeniyar fahimtar juna, da nufin saukaka kai ma’aikatan jinya na kasar Sin zuwa kasar Rwanda.
Ministan kiwon lafiya na kasar Rwanda Daniel Ngamije, ya bayyana a yayin bikin sanya hannu da ya gudana ranar Laraba cewa, “Mun yaba da wannan hadin gwiwa. Bayan shekaru 40 na hadin gwiwa a fannin likitanci tsakanin gwamnatin Rwanda da kasar Sin, a yau muna sanar da kara tsawaita wannan yarjejeniya zuwa shekaru biyar, saboda mun yaba da ayyukan da likitocin kasar Sin suka yi a kasarmu ya zuwa yanzu.
Jakadan kasar Sin dake kasar Rwanda Wang Xuekun ya bayyana cewa, kasashen Sin da Rwanda suna da dadaddiyar abokantaka, kuma hadin gwiwa a fannonin likitanci da kiwon lafiya, yana kara nuna kyakkyawar dadaddiyar alakar kasashen biyu, komai wahala komai dadi.
A shekarar 1982 ne, gwamnatin kasar Sin ta fara tura tawagar likitoci zuwa kasar Rwanda.
A cikin shekaru 40 da suka gabata, tawagogin likitocin kasar Sin 22 da likitocin kasar Sin sama da 270 sun karbi dubban daruruwan marasa lafiya, sun kuma yi aikin tiyata sama da 10,000 a kasar Rwanda. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp