Zamanintar da al’umma nasara ce da daukacin bil Adama ke sa ran cimmawa. Kasashen Sin da Vietnam na da yawan al’ummu da ya wuce biliyan 1.5. To ko mene ne ma’anar cimma nasarar zamanintar da su ga duniya?
Shugabannin kasashen biyu sun kai ga cimma matsaya daya game da sabuwar taswira a wannan bangare, yayin ziyarar aikin da Xi Jinping ya gudanar a kasar daga raneku 14 zuwa 15 ga watan nan. Ba ma kawai al’ummun kasashen biyu za su ci gajiya daga hakan ba, har ma matakin zai taka rawar gani wajen kiyaye zaman lafiya, da karko a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya, da samun ci gaba cikin hadin gwiwa, duk da cewa ana fuskantar sauye-sauye da kalubaloli a duniya.
- An Gudanar Da Harkokin Cudanya Da Musayar Al’adu Tsakanin Sin Da Malaysia A Birnin Kuala Lumpur
- Gwamnonin Nijeriya Sun Nuna Damuwarsu Kan Kashe-kashen Mutane A Filato
Yayin da shugabannin biyu suke zantawa, Xi Jinping ya gabatar da shawarwari 6, inda ya nanata wajibcin daga matsayin amincewa da juna a bangaren tsare-tsare, da kafa matakin tsaro mafi inganci, da kuma gaggauta hadin gwiwarsu a sabon matsayi, kana da kara dunkule al’ummun kasashen biyu, da gudanar da hadin gwiwa tsakanin bangarori daban-daban, kazalika da kara mu’ammala a bangaren aikin teku.
Wadannan shawarwari guda 6 sun samar da makoma mai haske ga zamamintar da al’ummun kasashen biyu da yawansu ya wuce biliyan 1.5, da ma kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya.
Hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren ciniki ingantaccen karfi ne na ingiza huldarsu. A cikin shekaru 20 a jere da suka gabata, Sin ta kai matsayin abokiyar ciniki mafi girma ga Vietnam, kuma Vietnam ta zama abokiyar ciniki mafiya girma ga kasar Sin a mambobin kungiyar ASEAN.
Yayin ziyarar aikinsa a wannan karo, Xi Jinping da Tô Lâm sun halarci bikin kaddamar da tsarin hadin gwiwar kasashen biyu wajen kafa layin dogo tsakaninsu. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun kulla yarjejeniyoyin hadin gwiwa har 45 tsakaninsu, ciki har da na kara tuntuba, da mu’ammala tsakaninsu, da fasahar AI, da aikin binciken kwastam, da cinikin kayayyakin aikin gona, da zaman rayuwar jama’a da sauransu.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ba da labarin cewa, ziyarar Xi a Vietnam a wannan karo, za ta gaggauta hadin gwiwar kasashen biyu a bangaren ciniki da tsarin samar da kayayyaki.
Idan mun yi hangen nesa a tarihi, ingantacciyar kyakkyawar makomar al’ummun biyu ta bai daya ta amfani al’ummun kasashen biyu da yawansu ya zarce biliyan 1.5, kuma tana kawowa duniya tabbaci, da dorewa da ake matukar bukata a halin yanzu duba da sauye-sauyen da ake fuskanta. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp