Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce ta damu da yadda kasar Amurka ke amfani da karfin gwamnati wajen danne kamfanonin kasar Sin.
Mao Ming, wadda sabuwar kakakin ma’aikatar ce, ta bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Litinin, inda ta nanata cewa, kamata ya yi kimiyya da fasaha ta zama hanyar amfanawa dukkan bil Adama, maimakon hanyar hanawa ko dankwafe ci gaban kasashe.
Ta ce rahotanni na cewa, gwamnatin Joe Biden tana tattauna batun hana kasar zubawa kamfanin kimiyya da fasaha na kasar Sin jari.
Ta ce amfani da batun tsaron kasa da kawo tsaiko da gangan ga dangantakar tattalin arziki da kimiyya da fasaha tsakanin Sin da Amurka, ya saba ka’idojin tattalin arzikin kasuwa da na kasa da kasa har ma da na cinikayya.
Haka kuma yana zagon kasa ga tabbacin da al’ummun duniya ke da shi kan yanayin kasuwanci a kasar, tana mai cewa, kaikayi zai koma kan mashekiya. (Fa’iza Mustapha)