A yau ne hukumar ‘yan sanda ta kasar Sin ta nuna rashin jin dadi da kin amincewa kan matakin karin harajin kwastam da kasar Amurka ta kakabawa kayayyakin Sin, bisa dalilin wai kasar Sin ce ta haddasa matsalar yaduwar magani na Fentanyl, da za a iya shan sa a matsayin wani nau’in miyagun kwayoyi, a Amurka.
Cikin wata sanarwar da hukumar ‘yan sanda ta Sin ta gabatar, an ce kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen hana yaduwar miyagun kwayoyi a duniya, kana ta dade tana kokarin hadin gwiwa da kasar Amurka a wannan fanni.
- NDLEA Ta Gargadi Iyaye Kan Bayyanar Alawar Ƙwaya A Kano
- Sin: Babu Wanda Zai Yi Nasara A Yakin Cinikayya Da Haraji
Ko da yake babu matsalar amfani da Fentanyl din a matsayin miyagun kwayoyi a kasar Sin, amma duk da haka kasar tana daukar matakin tsaurara manufofin amfani da maganin, da takaita fitar da shi zuwa kasuwannin duniya, a shekarar 2019, bisa bukatar taimako da kasar Amurka ta mika mata, da niyyar daukaka ra’ayin jin kai. Daga bisani, kasar Sin ba ta sake samun wani rahoto daga bangaren Amurka cewa an gano maganin Fentanyl da aka samar da shi a kasar Sin cikin kasuwannin Amurka ba.
Saboda haka hukumar ‘yan sanda ta Sin ta ce, kasar Amurka ita kanta ce ta haifar da matsalar yaduwar maganin Fentanyl, da ake yawan shan sa a matsayin wani nau’in miyagun kwayoyi, a cikin gidanta. Don daidaita matsalar, ya kamata kasar Amurka ta rage bukatar da ke akwai a cikin gidanta game da maganin, da karfafa hadin gwiwa tare da sauran kasashe ta fuskar dakile yaduwar miyagun kwayoyi, maimakon dora laifi kan sauran kasashe. (Bello Wang)