Sin ta tabbatar da adawar ta da matsayin Amurka na shirin dakatar da amfani da ababen hawa, dake hade da yanar gizo kirar kasar Sin, da sauran sassan manhajoji da bangarorin na’urori, wadanda ake shigarwa Amurka.
Da yake amsa tambaya da aka yi masa game da hakan a yau Laraba, kakakin ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ya ce tabbas wannan manufa ta Amurka na da nufin dakile wadannan nau’o’in ababen hawa kirar kasar Sin a Amurka bisa fakewa da batun tsaro.
Ya ce matakin daya ne daga matakan baya bayan nan da Amurka ke dauka da nufin gurgunta sashen masana’antun kirar motoci na Sin, matakan da suka hada da na kara haraji, da takunkuman sayen hajoji, da manufofin nuna wariya ta fuskar bayar da tallafi. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp