Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Zhang Jun, ya ce kasar sa na matukar adawa da siyasantarwa, ko amfani da batun yaki da ta’addanci a matsayin makamin cimma burin kashin kai, da yin fuska biyu, da mayar da wasu sassan saniyar ware.
Zhang Jun wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya ce ta’addanci kalubale ne da ya shafi duniya baki daya, kuma ba wata kasa guda daya dake da ikon shawo kan sa ita kadai.
Don haka a cewar sa, kamata ya yi dukkanin kasashen duniya su gane cewa, su al’umma guda ce mai makomar tsaro ta bai daya, don haka ya dace su aiwatar da cikakkun matakan yaki da ta’addanci bisa tanajin kudurorin MDD, da kwamitin tsaron majalissar, su murkushe dukkanin kungiyoyin ta’addanci, da daidaikun mutane da kwamitin tsaron MDD ya lasafta, cikin masu tallafawa ta’addanci. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp