Wani sabon rahoto da aka wallafa ya nuna cewa, ana hasashen ma’aikatan masana’antu masu kaifin basira da ake bukata a kasar Sin za su zarce miliyan 31 nan da shekarar 2035, bisa karuwar nemansu a wannan bangaren.
Rahoton da jami’ar Renmin ta kasar Sin ta wallafa game da daukar aiki da ake yayi na ma’aikata masu hazaka, a karkashin lura da sabon ingancin ma’aikata, wanda yake irinsa na farko a kasar Sin, na da nufin binciko rukunin kwararru na musamman ne masu tasowa, tare da bayar da misali ga masana’antu wajen tantancewa da daukar ma’aikata masu kwarewa, kamar yadda jaridar kimiyya da fasaha ta Science and Technology Daily ta ruwaito, a ranar Litinin din nan.
- Najeriya Da Sin Abokai Ne Dake Haifarwa Juna Da Alfanu
- Hukumar CDC Ta Karyata Barkewar Sabbin Cututtuka Masu Yaduwa A Sin
Rahoton ya kuma bayyana cewa, mutanen da ke rike da mukamai kamar su shugabannin tawagogin ma’aikata, da masu ayyuka na fasaha, da masu kula da ingancin aiki a masana’antun zamani, su ne ke zama kashin bayan kawo sauyi a bangaren masana’antun kere-kere.
Kazalika, rahoton ya bayyana cewa, ma’aikatan da kasar Sin ke bukata a masana’antun zamani sun kai akalla miliyan 25 tun a shekarar 2022. Bugu da kari, rahoton ya yi hasashen cewa ma’aikatan da ake bukata wadanda suka kammala digirin farko ko sama da haka za su karu daga kashi 28 cikin dari a shekarar 2022 zuwa kashi 57 nan da shekarar 2035. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)