A farkon makon nan ne rikicin Isra’ila da Falasdinu ya cika shekaru biyu cikin mummunan yanayin tashin hankali da ya yi matukar jan hankalin sassan kasa da kasa. Kuma har ya zuwa yanzu al’ummun Gaza na tsaka da fama da mummunan tasirin tashin hankali sakamakon ci gaba da hare-hare da dakarun Isra’ila ke kaddamarwa. Lamarin da ya haifar da asarar rayukan dubban fararen hula, da lalata dukiyoyi, da jefa dubun dubatar mazauna Gaza cikin yanayin matukar bukatar jin kai.
Alkaluman baya bayan nan sun nuna yadda tashin hankalin ya sabbaba rasuwar Falasdinawa sama da 67,000, tare da raba sama da miliyan daya da gidajensu. A wannan gaba da bukatun jin kai suka kai matsayin koli a Gaza, babban magataradar MDD Antonio Guterres, ya ayyana halin da zirin na Gaza ke ciki da “Babbar Akuba”.
Wani abun lura shi ne tun sake barkewar rikicin nan shekaru biyu da suka gabata, kasashe masu rajin wanzar da zaman lafiya a duniya, irinsu Sin da makamantansu, sun yi ta kiraye-kirayen a kai zuciya nesa, da komawa ga teburin shawarwari, da martaba dokokin kare hakkin bil’adama. Uwa uba da shawarar kafa kasashe biyu da kowa ya yi amanar ita ce hanya daya tilo ta kawo karshen wannan rikici baki daya.
Cikin darussan da wannan rikici ya tabbatar mana, akwai rashin tasirin amfani da karfin tuwo wajen warware duk wani rikici. Tabbas karfin soji kadai ba zai iya magance takaddama ko tashin hankali ba, ballantana ya wanzar da tsaro da walwalar bil’adama.
Muna iya ganin hakan a zahiri, idan mun lura da yadda Isra’ila ta nuna a fili cewa hare-haren da ta kwashe shekaru biyu tana kaiwa sassan Gaza za su iya kawo karshen barazanar da ta ce kungiyar Hamas ke haifar mata, amma sai ga shi daga karshe sakamako ya nuna akasin haka. Har yanzu dai sannu a hankali ana komawa ga shawarar da kasashe masu son zaman lafiya suka jima suna bayarwa, wato a rungumi tattaunawa, da dakarar da bude wuta, kana a shigar da agajin jin kai, da share fagen warware takaddamar ta hanyar siyasa.
A wannan gaba, ya wajaba a jinjinawa kasashe masu son zaman lafiya kamar Sin, da mafiya yawan kasashe masu tasowa, wadanda suka jima suna maraba baya ga cimma daidaito, da kawo karshen wannan tashin hankali da ya ki ci ya ki cinyewa, ciki har da sama da kasashe 150 membobin MDD da suka amince da Falasdinu a matsayin kasa.
Ko shakka babu, lokaci ya yi da za a kawo karshen tashe-tashen hankula, da samar da isasshen agajin jin kai ga masu bukata a Gaza, kana a komawa tattaunawar diflomasiyya ta kafa kasashe biyu masu cin gashin kai, a matakin karshe na ganin bayan wannan tashin hankali baki daya.
 
			




 
							








