A yau Litinin, a yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya, domin kara fahimtar rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, shugaban sashen fadakar da jamaa ta kwamitin ladabtarwa na kwamitin tsakiyar Jamiyyar Kwaminis ta Kasar Sin Wang Jianxin, ya bayyana cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta cimma nasara ta a-zo-a-gani a fannin yaki da cin hanci da karbar rashawa, amma, har yanzu aikin yakar cin hanci da karbar rashawa yana da sarkakiya matuka.
Wang Jianxin ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da kyautata tsarin yaki da cin hanci da karbar rashawa, domin kafa wani tsarin sa ido mai inganci daga dukkan fannoni bisa jagorancin JKS, ta yadda za a aiwatar da ayyuka masu nasaba da hakan yadda ya kamata. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)