Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya jagoranci taron manema labarai, inda ya amsa tambayoyin da aka yi masa game da taron tsarin tattaunawa kan hada-hadar cinikayya da tattalin arzikin Sin da Amurka.
Lin Jian ya nanata cewa, an yi wannan taro ne karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, inda suka kai ga matsaya daya wajen tabbatar da abin da shugabannin kasashen biyu suka cimma a tattaunawarsu ta wayar tarho a ran 5 ga watan nan da muke ciki da kuma ba da tabbaci ga ci gaban da aka samu a taron tattauna kan tattalin arziki da ciniki da suka gudana a watan Mayu a Geneva, kana da samun sabon ci gaba kan batun tattalin arziki da ciniki da suka tasa a gaba.
Jami’in ya ce, ba shakka Sin ta lashi takobin cika alkawarinta. Kuma duba da yadda bangarorin biyu suka kai ga cimma matsaya daya, dole ne su nace ga haka ba tare da tangarda ba, kana Sin tana fatan Amurka ta yi hadin gwiwa da ita don tabbatar da matsayar da shugabanninsu suka cimma, da kuma amfani da tsarin yadda ya kamata don ingiza hadin gwiwarsu ta hanyar kara tuntubar juna da kawar da bambancin ra’ayi. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp