Yayin taron manema labarai da ya gudana a Juma’ar nan a ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, kakakin ma’aikatar Mao Ning, ta bayyana yadda ta wakana, yayin zantawa ta wayar tarho tsakanin wasu manyan jami’an kasar Sin da na Amurka, inda ta ce bangaren Sin na bukatar tsagin Amurka ya martaba ikon mulkin kai, da tsaro, da moriyar ci gaban kasar, kana Amurka ta taka rawar gani wajen daidaita ci gaban alakarta da Sin, a maimakon yin akasin hakan.
Mao Ning ta jaddada cewa, batun yankin Taiwan jigo ne cikin manyan moriyar kasar Sin, don haka ya kamata Amurka ta nace ga sanarwar hadin gwiwar nan guda 3 da kasashen biyu suka amince da su, ta dakatar da samarwa Taiwan makamai, ta kuma cika alkawarin da ta dauka na kin mara baya ga yunkurin neman ‘yancin Taiwan.
- Wang Yi Ya Yi Jawabi A Liyafar Murnar Cika Shekaru 70 Da Fitar Da Ka’idoji 5 Na Zaman Tare Cikin Lumana
- Kumbon Chang’e-6 Na Kasar Sin Ya Tattaro Giram 1,935.3 Na Samfura Daga Yankin Duniyar Wata Mai Nisa
Kaza lika, jami’ar ta ce, batutuwan da suka shafi Xizang wato Tibet a bakin Turawa, su ma suna da nasaba da ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin, don haka wajibi ne Amurka ta daina bayyana goyon baya ga yunkurin masu neman ‘yancin Xizang, ta kuma kauracewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar Sin, ta fakewa da batutuwan da suka shafi Xizang.
Mao Ning ta kara da cewa, matsayar kasar Sin game da rikicin Ukraine ita ce rungumar gaskiya da adalci, kuma ya kamata bangaren Amurka ya dakatar da bata sunan kasar Sin, da kawo tsaiko ga hada-hadar tattalin arziki, da musayar cinikayya tsakanin Sin da Rasha. Ta ce, Sin na matukar adawa da yadda Amurka ke kakaba haramtattun takunkumai na kashin kai, da yanke hukunci kan wasu sassa ba bisa ka’ida ba, kuma Sin za ta kare daukacin hakkokinta bisa doka, da daukacin moriyar kamfanoni da daidaikun jama’arta. (Saminu Alhassan)