Assalamu alaikum, Malam Dan Allah ina da tambaya, Dan siyasa ya bani kudi na zabe shi na karbi kudin, kuma ban zabe shi ba, mene ne matsayin kudin in na ci?
Wa alaikum Assalam. To Gaskiya a fahimtata, in ka tabbatar ba za ka zabe shi ba, bai halatta ka amshi kudinsa ba, saboda Annabi (SAW) yana cewa: “Musulmai suna kan sharudansu” kamar yadda Bukhari ya ambace shi kuma Albani ya inganta shi a Irwa’ul galil hadisi mai lamba ta : 1743 ..
Sannnan kamar yadda ya haramta a ci dukiyar musulmai ba bisa hakki ba, haka ya haramta a ci dukiyar arne ba bisa hakki ba, ga shi kuma yaudara alama ce daga cikin alamomin munafuki, kamar yadda hadisai suka tabbatar.
Yana daga cikin ma’anonin dimukuraddiya zaben wanda Kake so, don haka babu bukatar boye-boye.
Allah ne mafi sani.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp