A jiya Talata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana cewa kasar Sin tana fatan gwamnatin Amurka mai shirin karbar ragamar mulki za ta nuna kamun ludayi mai kyau a huldar dake tsakanin Sin da Amurka.
Wang ya bayyana haka ne a yayin ganawarsa da wata tawaga bisa jagorancin babbar shugabar kwamitin kula da tsara manufofin hulda da kasashen waje na Amurka Susan Elliott.
- Dole Ne Amurka Ta Yi Watsi Da Matakin Babakere A Fannin Kimiyya Da Fasaha
- Zulum Ya Ƙaddamar Da Fara Aikin Titin Jirgin Ƙasa A Borno
Wang ya kara da cewa a ko da yaushe kasar Sin tana kokarin kyautata huldarta da Amurka bisa manufofin girmama juna, dorewar zaman lumana da kuma hadin gwiwar cin gajiyar juna a karkashin ko wane irin sauyi da aka samu a kasar ta Amurka.
Ya nuna cewa alkiblar da za a fuskanta a gaba dangane da huldar Sin da Amurka ta ta’allaka ce a kan zabin da Amurka ta yi, kana ya bayyana fatan bangaren na Amurka zai yi kokarin aiki da Sin ta yadda za su hadu a tsakiya.
A nata bangaren, tawagar wakilan na Amurka ta ce babban muradin kwamitin tsara hulda da kasashen waje na Amurka shi ne karfafa zumuncin Sin da Amurka, da cimma matsaya guda da kuma karfafa fahimtar juna. Kwamitin ya ce zai yi kokari kamar yadda ya saba yi a ko da yaushe wajen ganin ya sauke hakkin da ke wuyansa na zama gada da kuma kara kyautata alakokin Sin da Amurka. (Abdulrazaq Yahuza Jere)