Yau Labara, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta amsa tambayoyin da ‘yan jarida suka yi mata game da matsalar basusukan kasar Ghana.
Mao Ning ta nuna cewa, Sin a matsayinta na kasar dake rike da shugabancin kwamiti dake kula da matsalar basusukan kasar Ghana karkashin tsarin bai daya, tana daukar kwararan matakai don sa kaimi ga warware matsalar basusukan kasar Ghana yadda ya kamata. Ta nanata cewa, Sin na fatan ci gaba da taka rawa wajen ba da jagoranci da sulhuntawa don ingiza cimma shirin sake tsarin dake dacewa da ka’idar daukar mataki cikin hadin kai da sauke nauyin dake wuyanta bisa adalci.
- Sin Ta Mayar Da Martani Kan Yadda Amurka Ta Sayar Wa Taiwan Makamai
- Equatorial Guinea Za Ta Daukaka Huldarta Da Sin Zuwa Wani Sabon Matsayi, In Ji Shugaban Kasar
Dangane da sake zaben shugaba Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, Mao Ning ta ce, kasar Sin na taya shugaba Tshisekedi murna.
A game da batun rikicin Ukraine kuwa, Mao Ning ta ce tattaunawa da yin shawarwari su ne kawai hanyar da za a iya magance rikicin.
Dangane da batun Taiwan kuwa, Mao Ning ta ce, Taiwan wani yanki ne na kasar Sin da ba za a iya raba shi ba, kuma kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na mu’amala a hukumance tsakanin Amurka da yankin Taiwan na kasar Sin.(Amina Xu)