Za a gudanar da taron dandalin tattaunawa na Asiya na Boao na shekarar 2023 daga ranar 28 zuwa 31 ga watan Maris, a Boao na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, kana za a yi bikin kaddamar da taron a ranar 30 ga wannan wata.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a yau Litinin cewa, Sin tana fatan wakilai masu halartar taron za su yi amfani da wannan taro don tattaunawa kan neman ci gaba cikin lumana da samun moriyar juna ta hanyar hadin gwiwa, da kuma samar da shirin Boao na kyautata aikin sarrafa duniya da kara amfanawa jama’ar kasa da kasa.
Mao Ning ta kara da cewa, a halin yanzu, ana fuskantar sauye-sauye a yanayin samun bunkasuwa a kasa da kasa da yankuna. Taken taron na wannan shekara shi ne “Duniyar da ba ta da tabbas: Hada kai don daidaita kalubale, bude kofa da yin hakuri don inganta ci gaba”, wanda ya shaida ra’ayi iri daya na kasa da kasa na neman samun zaman lafiya da hadin gwiwa da kuma bunkasuwa tare. (Zainab)