A lokacin da na fara cin karo da rahotanni game da sabon yunkurin kasar Sin na samar da wata turba da za a gina kyakkyawar makoma ga rayuwar al’ummar duniya bai daya, da aka yi wa taken “Ziri Daya Da Hanya Daya”, abubuwa da yawa sun fado mun a rai game da manufar da ake son cimmawa musamman bisa la’akari da yadda galibin manyan kasashen duniya ke fakewa da guzuma su harbi karsana a Afirka. Amma da na tuna cewa, ba shi daga cikin manufofin kasar Sin mallake kasashe masu ‘yanci a fakaice ballantana a zahiri, sai na riya a raina cewa shirin zai yi nasara musamman a Afirka ko kuma na ce inda na fi wayau, Nijeriya.
Bayan Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar wa duniya da wannan tsari a shekarar 2013 a Tsangayar Nazarin Hulda a Tsakanin Kasashe da ke Birnin Moscow ta kasar Rasha da kuma huldodin difilomasiya da suka biyo baya, kasashenmu na Afirka sun yi na’am da abin, domin sun yi amannar cewa bisa sauye-sauyen da ake samu a wannan zamanin da kuma kalubalen da kan auko ba tare da shiri ba, akwai bukatar hadin gwiwa na bai daya saboda babu wata kasa daya tilo da za ta iya magance matsalolin da suka shafi rayuwar jama’a ita kadai.
Kasashenmu na Afirka suna bukatar kayan more rayuwa da sahihan abokan hulda na gaskiya don su iya cike gibin da suke da shi ta wannan bangaren. Shi ya sa shawarar ta “Ziri Daya Da Hanya Daya” ta zamo tamkar tudun-mun-tsira gare su. Kamar yadda Shugaba Xi ya yi bayani, babban burin shawarar ita ce gina al’umma mai kyakkyawar alaka da juna da za ta ci gaba da rayuwa cikin dawwamammen zaman lafiya da tsaro da amfanar da juna da kyautata difilomasiyya ta hanyar girmama juna bisa adalci.
Nijeriya a matsayin Giwar Afirka, ba a bar ta a baya ba, domin tana amfana sosai da kwangilolin hadin gwiwa na samar da kayan more rayuwa a tsakaninta da Sin. Bari mu faro da bangaren sufuri, Nijeriya tana da tarihin sufurin jiragen kasa tun a zamanin mulkin mallaka, amma daga baya harkar ta tabarbare. Aikin layin dogon da aka yi na tsakanin Kaduna da Abuja da ya kai kimanin Dala Miliyan 500 ya zama tubalin farfado da sashen na jiragen kasa. Haka nan, kwangilar layin dogo na Birnin Abuja ta kara kawo ci gaba a birnin a matsayinsa na Babban Birnin Tarayyar Nijeriya. Babban aikin layin dogo da ya tashi daga Legas zuwa Ibadan wani karin ci gaba ne ga Nijeriya.
Har ila yau, a sakamakon shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”, Nijeriya ita ce ta farko a yammacin Afirka da ta samu sufurin jirgin kasa mai amfani da lantarki a Jihar Legas. Kamar yadda masharhanta suka yi bayani, yanzu haka layin dogon yana taimakawa wajen habaka sufuri da bunkasa tattalin arziki a jihar wacce take zama babbar cibiyar hada-hadar kasuwanci ta Nijeriya. Akwai sauran manyan ayyukan layin dogo da Nijeriya ta ci moriyarsu daga Sin da suka kunshi na Legas zuwa Kalaba mai tsawon kilomita 1402 da wanda ya tashi daga Abuja zuwa Itakpe ya dangana da Warri da sauransu.
Ta bangaren amfani da fasahar sadarwar zamani kuwa, akwai yarjejeniyar da Nijeriya ta cimma da kasar Sin ta samar da wasu manyan ginshikan fasahar ICT a kan kudi Dala Miliyan 100, sai batun samar da wutar lantarki ta ruwa daga tashar Zungero da lamuninsa ya kai Dala Miliyan 984.3
A lokacin da na samu damar ziyartar kasar Sin a shekarar 2018, mun ziyarci shalkwatar Kamfanin China Habour Engineering Company (CHEC). Daga cikin abubuwan da na tattauna da shugaban reshen kamfanin a Nijeriya, Mista Jason, har da batun aikin titin da ya tashi daga Abuja zuwa Keffi ya nausa Makurdi da aka ba kamfanin kwangilar yi. Nijeriya ta ci moriyar wannan aiki baya ga Tashar Teku Mai Zurfi ta Lekki wanda duk kamfanin ne ya aiwatar.
Wani bangare na ci gaba da har ila yau wannan shawara ta “Ziri Daya Da Hanya Daya” ta haifar shi ne ayyukan fadada manyan filayen jiragen sama na Abuja, Kano, Legas da kuma Fatakwal. Masana sun kiyasta cewa ana sa rai aikin ya kara yawan fasinjojin da ke kai-komo a filayen jiragen daga miliyan 20 zuwa miliyan 50. Sannan ayyukan yi su bunkasa daga 60,000 zuwa miliyan 1.5. Tuni aka kaddamar da aikin tare da fara cin moriyarsa.
Annobar COVID-19 wata cuta ce da ta shiga tarihin duniya da ba za a manta da ita ba. A yayin da take ganiyarta, wannan shawara ta “Ziri Daya Da Hanya Daya” ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile ta a Nijeriya. Duk da cewa kowace kasa ta yi fama da kanta, amma kasar Sin ba ta bar kawayenta ba. Na tuna lokacin da Ministan Kiwon Lafiya na Nijeriya, Dr Osagie Ehanire ya yi godiya ga Sin bisa tallafin kayan aiki da ta bai wa Nijeriya ta hannun Jakadanta na kasar, Mr Zhou Pingjian, wanda babban sakataren ofishin jakadanci na uku, Li Guanjie ya wakilta. Baya ga kayan aiki, hatta kwararrun likitoci, Sin ta aike da su Nijeriya domin su taimaka wa kasar wajen dakile annobar. Har ila yau, kamfanonin Sin da ke ayyukan kwangiloli a Nijeriya sun yi gamayya tare da samar da kayan riga-kafi na miliyoyin Naira domin taimaka wa yaki da cutar har aka samu nasara. Shi ya sa tsakanin Sin da Nijeriya sai godiya.
Tabbas shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya” ta bude sabon babin ci gaba ba ga Nijeriya ba kawai har da duniya baki daya musamman idan aka yi la’akari da yadda cinikayya ta bunkasa a tsakanin Sin da kasashen da ke cikin shirin, daga Dala Tiriliyan 1.4 a 2013 zuwa Dala Tiriliyan 2.07 a 2022. (Abdulrazaq Yahuza)