Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta jaddada a yau Litinin 23 ga wata cewa, kasarta na aiwatar da hadin-gwiwa tare da sauran kasashe masu tasowa a fannin hada-hadar kudi da zuba jari, ba tare da gindaya musu sharadin siyasa ba.
Rahotannin sun ruwaito cewa, kwanan nan ne fadar White House ta kasar Amurka ta ce, kasar Sin na gudanar da harkokin hada-hadar kudi ala tilas kuma marasa dorewa tare da kasashe masu tasowa daban-daban. Don haka ita Amurka za ta bullo da wani amintaccen shiri na daban.
- An Yi Bikin Kaddamar Da Gasar Wasannin Motsa Jiki Ta Mutane Masu Bukata Ta Musamman Ta Asiya A Hangzhou
- Me Ya Sa Kasar Sin Ke Son Ganin Nijeriya Ta Samu Ci Gaba Mai Inganci?
Game da wannan batu, Mao Ning ta ce, babu gaskiya a cikin wadannan kalaman Amurka ko kadan. Kasar Sin na gudanar da harkokin hada-hadar kudi tare da kasashe masu tasowa, daidai bisa ka’idojin kasa da kasa da manufar samar da rance mai dorewa, kana, a bisa ra’ayin kansu ba tare da gindaya musu sharadin siyasa ba. Kada a ce kasar Sin ta tilasta musu yin haka.
Jami’ar ta kuma ce, tun daga shekarar da ta gabata, har zuwa yanzu, Amurka tana kara kudin ruwa da ba’a taba ganin irinsa ba a tarihi, al’amarin da ya kara jefa kasashe masu tasowa da dama cikin mawuyacin hali na biyan basussuka, har ma kasuwannin kudaden duniya na tangal-tangal. A matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a duniya, Amurka na da alhakin taimakawa kasashe masu tasowa, don haka, ana fatan Amurka za ta bullo da wani shiri na zahiri, maimakon shafawa sauran kasashe bakin fenti. (Murtala Zhang)