A duk lokacin da mutum ya ratsa manyan hanyoyin mota na kasar Sin, musamman masu bin filaye masu fadi da yankunan bakin ruwa, zai rika cin karo da manyan wurare da aka kebe domin samar da lantarki ta karfin iska, inda ake iya ganin manyan turakun nan masu kama da babbar fanka na juyawa sannu a hankali a sama, wanda hakan ke alamta yadda kasar Sin ta zage damtse wajen gaggauta sauya akala, zuwa cin gajiya daga nau’o’in makamashi marasa gurbata yanayi.
Wasu alkaluma sun nuna cewa, a rubu’in farko na shekarar bana, karfin lantarki da Sin ke samarwa daga karfin iska, da na hasken rana ya kai kilowats biliyan 1.482, adadin da ya haura wanda ake samu daga tururin zafi a karon farko a tarihin kasar.
- Mun Shirya Fuskantar APC Domin Ceto Talakawa – Abubakar Malami
- Dutsen Da Amurka Ta Jefa Ya Fado Kasa
Yayin da ake ta fadada kayayyakin samar da lantarki ta sabbin hanyoyi marasa gurbata muhalli a kasar Sin, hanyoyin samar da shi daga iska da hasken rana za su ci gaba da karuwa a shekaru masu zuwa, wanda hakan ke nuni ga babban sauyi da kasar ke samu a tsarin samar da makamashi baki daya.
Baya ga moriya daga makamashi, su ma kamfanonin dake taka rawar gani a wannan fanni na kara bunkasa, zuwa cibiyoyi mafiya inganta fasahohinsu a duniya, ta fuskar kirkire-kirkire da sarrafa hajoji, inda sannu a hankali suke sauyawa daga masu dogaro da manyan fasahohin waje zuwa na kan gaba a duniya wajen fitar da kayayyakin bukata a fannin samar da lantarki daga iska da hasken rana.
Ko shakka babu, sauyin akalar samar da makamashi na kasar Sin na kara tabbatar da dorewar manufofin kasar da aiki tukuru. A tsawon shekaru, Sin ta ci gaba da tsara manufofi, da aiwatar da su daki-daki, ta yadda ta kai ga bunkasa sauyin da ake fata a fannin makamashi. Babban burin dai shi ne gina tsarin samar da isasshen makamashi mai tsafta, mai karancin fitar da iskar carbon mai dumama yanayi kuma marar hadari. Tare da raba ribar wannan gajiya da sauran sassan kasa da kasa.(Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp