Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bukaci gwamnatin kasar Japan da ta bayar da cikakken hadin kai, don samar da tsari mai inganci, mai zaman kan sa na tsawon lokaci, wanda zai baiwa sassan kasa da kasa, da hadin gwiwar kasashe makwaftan kasar damar sanya ido ga batun ruwan dagwalon nukiliyar tashar Fukushima Daiichi da Japan din ke zubarwa a teku.
Mao Ning, wadda ta bayyana hakan a Juma’ar nan, yayin da take amsa tambayoyin manema labarai game da ci gaba da tattaunawa tsakanin bangarorin 2, tun bayan da gwamnatin Japan din ta fara zubar da ruwan dagwalon cikin teku shekara guda da ta gabata, kuma Japan din ta bukaci Sin ta dage haramcin shigar da albarkatun abincin ruwa na Japan cikin kasar ta Sin.
- Kasar Sin Ta Harba Sabon Tauraron Dan Adam Na Sadarwa
- Yadda Al’ummar Da Ke Zaune Da ‘Yan Bindiga Ke Rayuwa A Zamfara
Mao, ta ce ba tare da tuntubar kasashe makwaftanta ba, Japan ta yi gaban kan ta, inda ta fara zubar da dagwalon nukiliyar na tashar Fukushima cikin teku, lamarin da ka iya jefa sauran sassan duniya cikin hadari. Kaza lika, matakin nuna rashin sanin ya kamata ne, bai kuma dace da dokokin kasa da kasa ba, kana ya sabawa ka’idojin alakar kasashe makwafta.
Mao ta kara da cewa, abu ne da ya dace da doka, da hankali, kana wajibi ne Sin da sauran kasashe su dauki matakan kandagarki don kare ingancin abinci, da lafiyar al’umma, sakamakon fara zubar da wancan dagwalo cikin teku. (Saminu Alhassan)