Kafofin watsa labaru na kasashen waje da dama ciki har da jaridar Financial Times da mujallar The Economist da sauransu sun mai da hankali kan yadda kasar Sin ta zama kasa mai karfin yin kirkire-kirkire, inda suka yi bayanin cewa, kasar Sin ta sauya daga zama cibiyar masana’antun duniya zuwa wurin yin gwaji na duniya, kuma kasashen yammacin duniya suna bukatar yin kokari don samun ci gaba kamar Sin.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana a yau Jumma’a 5 ga wannan wata cewa, hakikka yin kirkire-kirkire ya zama muhimmin abu yayin da Sin take kokarin raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma. A shekarun baya-baya nan, Sin ta samu manyan nasarori a fannin kimiyya da fasaha da kuma yin kirkire-kirkire, matsayinta a duniya a fannin kirkire-kirkire ya karu zuwa mataki na 10 a shekarar 2025 a maimakon na 34 a shekarar 2012.
Lin Jian ya bayyana cewa, ana fuskantar yin takara da juna yayin da ake yin kirkire-kirkire, amma burin yin kirkire-kirkire ba samun nasara a cikin takara ba ne. Kasar Sin tana yin kirkire-kirkire tare da bude kofa ga kasashen waje, da kuma neman samun moriyar juna a duniya. Kasar Sin tana son more fasahohi da kirkire-kirkire tare da duniya, da kara yin hadin gwiwa da bude kofa ga kasashen waje don samun ci gaba tare, ta haka za a amfanar da dukkan dan Adam ta hanyar kirkire-kirkire. (Zainab Zhang)














