Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin na maraba da abokai daga kasashen waje, da suka kara mayar da hankali da ziyartar kasar. Lin Jian ya yi tsokacin ne yayin taron manema labarai na Talatar nan, lokacin da aka bukaci ya yi karin haske game da matakin kasar Sin, na kara sassauta manufarta ta yada zangon matafiya ba tare da biza ba.
Lin Jian ya kara da cewa, a baya-bayan nan, Sin ta cimma nasarar fitar da cikakken tsarin kawar da bukatar biza tare da kasashe 26, yayin da ta amince da dauke bukatar biza kan wasu kasashen 38 da suka hada da Faransa da Jamus, kana ta amince da baiwa al’ummun wasu kasashen 54 damar shiga Sin don yada zango ba tare da bukatar biza ba, baya ga jerin kasashe da yankuna 157, da Sin din ta kammala yarjejeniyar kawar wa juna biza tare da su.
A yau Talata 17 ga watan nan, kasar Sin ta sanar da cikakkiyar manufar kara sassauta damar yada zangon matafiya ba tare da biza ba, tare da tsawaita iznin zama ga matafiya daga kasashen waje da suka yada zango a kasar, daga matakin sa’o’i 72, da na 144, zuwa sa’o’i 240 ko kuma kwana 10. Kaza lika, an kara yawan mashigi 21, a cikin wadanda za a iya shiga ko fita kasar ta cikinsu ba tare da biza ba, wanda hakan zai baiwa karin baki ‘yan kasashen waje damar balaguro ta cikin sassan kasar. (Saminu Alhassan)