Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Litinin cewa, kasar Sin tana maraba da karin abokai daga kasa da kasa su shigo kasar su bude ido, tare da kai kayayyaki kirar Sin masu inganci zuwa kowane iyali da amfanawa karin jama’ar kasa da kasa.
Rahotanni sun ce a sakamakon samar da saukin shigowa kasar Sin don yawon shakatawa da kuma mayar da kudin haraji ga baki masu yawon shakatawa, an kara samun zuwan masu yawon bude ido daga kasa da kasa cikin kasar tare da kara kashe kudi. Yawan rajistan da aka yi na shigowa kasar Sin domin yawon bude ido a yayin hutun ‘yan kwadago ya karu da kashi 173 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, inda masu bude ido daga kasashen waje da dama suka dauki manyan akwatuna domin yin sayayya a kasar Sin.
- Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
- Bai Dace A Mika Wuya Ga Wanda Ya Nuna Fin Karfi Da Matakan Haraji Ba
A gun bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin wanda aka fi sani da Canton Fair da aka gudanar a kwanakin nan, yawan masu sayayya daga kasashen waje ya karu da kashi fiye da 20 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, kana bikin baje koli ya jawo masu sayayya daga kasashe da yankunan duniya fiye da dubu 60.
Guo Jiakun ya bayyana cewa, a ranar 26 ga wannan wata, hukumomin Sin masu ruwa da tsaki sun gabatar da sabbin matakan mayar da kudin haraji ga baki masu yawon bude ido, lamarin da ya kyautata manufar mayar da kudin haraji tun daga lokacin sayayya da kawo sauki ga baki masu sayayya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp