Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce rundunar sojin ’yantar da jama’ar kasar Sin ta PLA yankin gabas, ta aiwatar da matakan da suka kamata, lokacin da jirgin ruwan yaki na Amurka samfurin “USS Higgins (DDG-76)”, da na ba da kariya na Canada mai lakabin “HMCS Vancouver”, suka ratsa mashigin tekun Taiwan.
Lin Jian ya bayyana hakan ne a Litinin din nan, yayin taron manema labarai, game da tambayar da wani dan jarida ya gabatar don gane da batun a jiya Lahadi.
- Gwamnan Kano Ya Taya Kwankwaso Murnar Cika Shekara 68 Da Haihuwa
- Fashewar Tankar Man Fetur A Jigawa: Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Haura 180
Jami’in ya kara da cewa, Sin na matukar bayyana adawa da duk wani mataki da wata kasa za ta dauka na takala, da barazana ga ikon mulkin kai, da tsaro ta fakewa da ‘yancin shawagin jiragen ruwa.
A bangaren sojan kasar Sin, mai magana da yawun rundunar sojin ’yantar da jama’ar kasar Sin PLA ta yankin gabas, babban-kanar Li Xi ya bayyana a jiya Lahadi cewa, jirgin ruwan yaki mai tarwatsawa na Amurka mai lakabin “USS Higgins (DDG-76)” da jirgin ruwa mai ba da kariya na Canada mai lakabin “HMCS Vancouver” sun ratsa mashigin tekuTaiwan tare da kara ta’azzara yanayin da ake ciki.
Rundunar soja na Sin ta tura sojojin teku da sama don sa ido da yin gadi kan ziyararsu daga farko zuwa karshe bisa doka. Matakin da wadannan kasashen biyu ke daukawa na keta zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan wuri. Rundunar da Sin ke jibge a wurin za ta ci gaba da kara karfin yin gadi, don kare ’yancin kasar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin wurin. (Masu Fassarawa: Saminu Alhassan, Amina Xu)