Hukumar kula da ayyukan kumbuna masu dauke da ma’aikata ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana cewa, an shirya harba kumbon binciken duniyar wata na Chang’e-7 a lokacin da ya dace.
Hukumar CMSA ta bayyana cewa, an yi jigilar hadadden kumbon na binciken wata na Chang’e-7 da rokar daukarsa ta Long March-5 Y14 a tsaye, zuwa wurin harbawa da ke cibiyar harba kumbuna ta Wenchang, a lardin Hainan na kudancin kasar Sin, a yau Laraba.
Za a harba kumbon na Chang’e-7 ne da nufin samun gagarumar nasara a fannonin fasahohi masu muhimmanci da dama, kamar yadda hukumar ta CMSA ta bayyana, kana ta ce kumbon zai yi amfani da cikakken tsarin gudanar da binciken gano abubuwa. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahauza Jere)














