ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Sin Na Son Taka Rawar Gani Wajen Maido Da Kwanciyar Hankali A Yankin Gabas Ta Tsakiya Cikin Sauri

by CGTN Hausa and Sulaiman
6 months ago
Sin

Yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun, ya shirya taron manema labarai na yau da kullum da aka saba yi.

Yayin da yake magana dangane da rawar da Sin ta taka a rikicin Iran da Isra’ila, Guo Jiakun ya ce, bayan da rikicin ya barke, shugaba Xi Jinping ya fayyace matsayin kasar Sin kan lamarin, kuma kasar ta ci gaba da mu’amala da kasashen Iran, Isra’ila, Masar, Oman, da sauran bangarori, inda ta yi kira da su dauki matakai cikin gaggawa don sa kaimi ga kwantar da halin da ake ciki yanzu.

  • Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
  • Ba Za Mu Yarda A Yi Mana Ƙarfa-ƙarfa Ba – Ayatollah Ya Gargaɗi Amurka

Bangaren Sin na son ci gaba da yin hadin gwiwa tare da sauran kasashen duniya don maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya cikin sauri.

ADVERTISEMENT

Bugu da kari, kasar Sin ta yi kira ga bangarorin da rikicin ya shafa musamman Isra’ila, da su sanya moriyar jama’ar kasashen yankin a gaba, da gaggauta tsagaita bude wuta, da sassauta halin da ake ciki yanzu.

Dangane da batun da wasu kafofin yada labarun Amurka suka sanar cewa jami’an Amurka na shirin kai wani hari kan Iran, Guo Jiakun ya ce, Sin na adawa da amfani da karfin tuwo a kan huldar kasa da kasa. Kuma ya kamata kasashen duniya, musamman ma manyan kasashe masu tasiri, su tsaya tsayin daka kan adalci da kuma sauke nauyin dake wuyansu, ta yadda za a samar da yanayi na inganta tsagaita bude wuta da kawo karshen yakin.

LABARAI MASU NASABA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

Dangane da sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar na cewa za ta maido da yin tambayoyi ga dalibai kafin a ba su biza kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta lura da batun, kuma tana fatan Amurka za ta aiwatar da kalaman shugaba Trump na maraba da daliban kasar Sin da su zo Amurka don yin karatu.

Dangane da wani rahoto da wata cibiyar bincike ta kasar Switzerland ta fitar, inda ta bayyana cewa, matsayin karfin yin takara na yankin Hong Kong na Sin ya karu zuwa matsayi na uku a duk fadin duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan na nuni da matsayin Hong Kong na musamman da kuma alfanun da ake da shi, da kuma tabbatar da ci gaban manufar “Kasa daya, mai tsarin mulki biyu”.(Safiyah Ma)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara
Daga Birnin Sin

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka
Daga Birnin Sin

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025
Next Post
Sin Ta Fadada Matakin Rage Haraji Ga Kasashe Masu Raunin Tattalin Arziki

Sin Ta Fadada Matakin Rage Haraji Ga Kasashe Masu Raunin Tattalin Arziki

LABARAI MASU NASABA

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025
Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.