Yayin da duniya ke fuskantar manyan kalubalolin dake barazana ga rayuwa, da kiwon lafiyar bil adama, daya daga manyan matsalolin da ake fatan shawo kan su shi ne sauyin yanayi.
A bana, kasashe da dama sun fuskanci tsananin zafi dake barazana ga rayuwar al’ummun su, wanda masana da dama ke alakantawa da karuwar dumamar yanayi. Masharhanta da yawa na ganin manyan kasashen duniya sun yi kasa a gwiwa, wajen sauke nauyin dake wuyan su, game da sauya akala daga manfani da nau’o’in makamashi masu dumama yanayi, zuwa sabbin makamashi masu tsafta.
Sai dai a gefe guda, kasar Sin ta yi nisa wajen aiwatar da manufofinta na dakile dumamar yanayi, inda a baya bayan nan mahukuntan kasar ke cewa, nan da shekarar 2030, kasar za ta kai kololuwar fitar da sinadarin carbon mai dumama yanayi, daga nan kuma adadinsa ya fara raguwa, zuwa yanayin da zai kai ga kawo karshen tasirinsa baki daya.
Ko shakka babu wannan labari ne mai faranta rai, domin kuwa a matsayin ta na kasa mai ci gaban masana’antu, cimma wannan buri zai ba da gagarumar gudummawa, a fannin rage dumamar yanayi a duniya baki daya.
Abun fatan dai shi ne, sauran manyan kasashen duniya, musamman masu ci gaban masana’antu, za su zage damtse wajen sauke nauyin dake wuyan su, a fannin rage tashoshin sarrafa makamashi daga abubuwa masu haifar da dumamar yanayi, su kuma karkata ga amfani da nau’o’in makamashin da ake iya sabuntawa, domin kuwa daukacin bil adama na rayuwa ne cikin wannan duniya kwaya daya, don haka kare muhallin duniya, nauyi ne kan dukkanin al’ummun duniya baki daya. (Saminu Hassan)