Ofishin jakadancin kasar Sin a kasar Jordan da kungiyar agaji ta Hashemite ta Jordan din, sun gudanar da bikin tura kayayyakin agaji zuwa zirin Gaza a jiya Talata.
Za a tura tallafin wanda Sin ta samar ne daga Jordan zuwa Gaza ta iyakokin kasa. Kuma za a tura tallafin wanda ya kunshi kunshin abinci 60,000, cikin kashi 6. Da zarar kashin farko na kayayyakin da suka hada da kunshin abinci 12,000 sun isa Gaza, za a mika su hannun shirin samar da abinci na duniya (WFP) da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Palasdinu da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki.
Yayin bikin tura kayayyakin, jakadan Sin a Jordan Chen Chuandong, ya ce a matsayinta na kawar al’ummar Palasdinu, kasar Sin ta tura kayayyakin agaji sau da dama zuwa Gaza, kuma za ta ci gaba da kara tallafawa Palasdinawa. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)