Ma’aikatar kula da muhalli da halittun ruwa ta kasar Sin ko MEE ta bayyana a jiya Juma’a cewa, kasar Sin ta samu ci gaba sosai wajen kiyaye muhallin halittun ruwa na muhimman kogunan kasar, tare da kyautata ingancin ruwan kasar a rabin farkon bana.
Wani jami’in MEE Huang Xiaozeng, ya shaida wa taron manema labarai cewa, adadin koguna na fadin kasar da ke da ingantacciyar ruwa ya kai kashi 89.4 a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 1.5 cikin dari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
- ‘Matsalolin Da Ke Kawo Cikas Ga Shirin Samar Da Wutar Lantarki’
- Sabbin Sassan Da Ke Ingiza Bunkasuwar Sin Sun Kara Samun Kuzari
Huang ya kara da cewa, wannan adadi ya zarce manufar da aka tsara a cikin shirin raya kasa na shekaru biyar biyar na 14 wato daga shekarar 2021 zuwa ta 2025, da kashi 4.4 cikin dari.
Daukar kogin Yangtze a matsayin misali, Huang ya ba da rahoton cewa, kashi 98.5 cikin dari na wuraren da ake sa ido a yankunan kogin sun samu kyakkyawan ingancin ruwa a shekarar 2023, wanda ya karu da kashi 0.4 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin bara.
Bugu da kari, adadin nau’ikan kifaye na asali da aka samu a cikin kogin Yangtze ya karu zuwa 227, sama da nau’ika 34 da ake da su a shekarar 2022. Yawan nau’in halittun ruwa da ake karewa a kasar ya karu zuwa 14 a shekarar 2023, wato karuwar uku idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. (Mai fassara: Yahaya)