An yi bikin mika tallafin kayayyakin jinya da Sin ta samarwa Habasha, a jiya Laraba, a asibitin Tirunesh-Beijing dake Addis Ababa.
Tawagar jami’an lafiya ta 25 ta kasar Sin mai tallafawa Habasha ce ta samar da tallafin kayayyakin jinyar ga wannan asibitin. Kayayyakin sun hada da na’urorin jinya da magunguna da kayayyakin aikin likita da na gwaje-gwaje da sauransu. Shugaban tawagar Liu Junying ya bayyana yayin mika tallafin cewa, kayayyakin jinya da Sin ta bai wa Habasha na kunshe da dankon zumunci mai zurfi na Sinawa, lamarin da ya bayyana niyyar kasashen biyu ta hadin gwiwa a bangaren kiwon lafiya da dakile matsaloli da kalubaloli tare.
A nasa bangare, shugaban asibitin Eshetu Tadele ya ce, “Ba kayayyakin tallafi kadai Sin ta ba mu ba, abin mafi muhimmanci shi ne mambobin tawagogin lafiya daban-daban sun hada hannu da mu wajen bayar da horo kan fasahar jinya da kiwon lafiyar al’ummar Habasha.” Ya kuma bayyana godiya ga taimakon da Sin ta bai wa kasarsa. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp