Kasar Sin ta mikawa hukumar yaki da bala’u ta kasar Somaliya, tallafin dalar Amurka 150,996, don amfani da su wajen samar da kayayyakin jin kai ga ’yan kasar, wadanda bala’u daga indallahi suka aukawa.
A jiya Lahadi, shugaban hukumar yaki da bala’u a Somaliya ko SoDMA a takaice, Mahamud Moallim Abdulle ya jinjinawa tallafin na kasar Sin, lokacin da yake maraba da taimakon, yana mai jaddada dankon zumuncin dake tsakanin Somaliya da Sin a tsawon lokaci.
Abdulle, wanda ya yi tsokacin a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar, ya kara da cewa, gwamnati da al’ummar Somaliya suna da tarihi na kyakkyawar alaka da goyon baya tsakaninsu da Sin, kuma ba wannan ne karon farko da Sin din ke baiwa kasarsu irin wannan tallafi ba.
A nasa tsokacin kuwa, jakadan kasar Sin a Somaliya Fei Shengchao ya ce, tallafawa masu fama da bala’u, alama ce dake tabbatar da aniyar kasar Sin ta karfafa hadin gwiwa da Somaliya.
Fei ya kara da cewa, “Kamar yadda muka sani, Sin da Somaliya na da dadadden tarihi mai karko, wanda ka iya jure duk wani sauyi a harkokin shiyyoyi ko na kasa da kasa.”
Tallafin na Sin dai na zuwa ne yayin da MDD ke gargadin cewa, al’ummun Somaliya da suka rasa matsugunansu, da makiyaya, na iya fuskantar kamfar abinci na tsawon lokaci a yankunan kasar da suka fi fuskantar yanayin fari na baya bayan nan.(Saminu Alhassan)