A yau Talata ne kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya ce Sin na matukar nuna bacin rai, tare da adawa mai tsanani, game da matakin Amurka na sayarwa yankin Taiwan na Sin makamai.
Wu Qian, ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga sanarwar cinikayyar makamai ta kudi har dala miliyan 300 ga yankin Taiwan, wanda hukumar hadin gwiwar harkokin tsaro ta Amurka ko DSCA, dake karkashin ma’aikatar tsaron Amurka ta fitar.
- Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Zaben Tambuwal Da Wamakko A Matsayin Sanatoci
- Xi Ya Saurari Rahoto Daga Manyan Jami’an Gwamnatocin HK Da Macao
Wu ya ce wannan cinikayya, ta yi matukar sabawa manufar nan ta kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwar hadin gwiwa 3, da kasashen Sin da Amurka suka amincewa, musamman ma ta ranar 17 ga watan Agusta.
Ya ce matakin na Amurka, ya yi matukar keta hurumin kasar Sin na kasancewa kasa mai ‘yanci, da tsaron kasar, kana barazana ce ga zaman lafiya da daidaito a zirin Taiwan. Kaza lika hakan zai aike da gurgun sako ga ‘yan aware, dake fafutukar ballewar yankin na Taiwan. (Mai fassara: Saminu Alhassan)