Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ya yi kira ga Amurka da ta dakatar da fakewa da batun zargin yaduwar sinadarin fentanyl, a matsayin dalilin kakabawa Sinawa takunkumi, ko yanke hukuncin shari’a, ko sanya ladan kamo Sinawa, ko bata sunan kamfanonin su.
A ranar Juma’a ne dai ma’aikatar shiri’ar Amurka, ta bayyana samun wasu kamfanonin kasar Sin, tare da ma’aikatan su da laifi sarrafawa, da kuma rarraba sinadarin na fentanyl, wanda ake amfani da shi wajen harhada miyagun kwayoyi a cikin kasar.
Kakakin ma’aikatar wajen Sin din ya ce jami’an tsaron Amurka, sun danawa wasu Sinawa tarko a wata kasa ta daban, tare da yanke musu, da wasu kamfanoni da suke yiwa aiki hukunci. Wanda hakan ya sabawa doka, kuma mataki ne na kame ba bisa ka’ida ba, da kakaba tukunkumi na kashin kai, wanda ya sabawa doka baki daya. Don haka dai bangaren Sin ke cewa matakin ya keta hakkokin bil Adama na Sinawan da aka tsare, da ma moriyar kamfanonin da batun ya shafa.
Daga nan sai kakakin ma’aikatar wajen Sin din ya ce kasar sa na matukar Allah wadai da wannan mataki na Amurka, ta kuma gabatar da korafi mai karfi ga tsagin Amurka kan batun. (Mai fassarawa: Saminu Alhassan)