Yau Lahadi, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida dangane da matakin Amurka na soke karin haraji kan wasu kayayyaki da ake shigarwa kasar.
Kakakin ya ce, wannan wani karamin mataki ne da Amurka ta dauka don gyara kuskuren da ta yi na daukar matakin kare-karen harajin fito kan hajojin da ake shigarwa kasar bisa radin kai. Ya ce, Amurka ta gabatar da abin da ake kira “kudurin haraji” ta hanyar tsarin zartaswa, matakin da ba wai kawai ya saba wa ka’idojin tattalin arziki da cinikayya ba, har ma ya yi watsi da hadin gwiwa da alakar samar da kayayyaki tsakanin kasashen duniya.
Sin ta bukaci Amurka da ta ji muryoyin kasashen duniya da na cikin gida, da daukar wani babban mataki na gyara kuskuren da ta yi, da kuma soke mummunan matakin da ta dauka na kare-karen harajin fito kan hajojin da ake shigarwa kasar.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp