Yau Litinin, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Lin Jian ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum.
Yayin taron, Lin Jian ya bayyana cewa, hakikanin yanayi ya shaida cewa, babu wanda zai yi nasara a yakin haraji da yakin cinikayya, matakin haraji da Amurka ta dauka zai lalata kanta da sauran kasashe. Sin ta bukaci bangaren Amurka da ya yi watsi da matakinta na matsawa sauran kasashe lamba, da kuma warware matsaloli ta hanyar tattaunawa bisa tushen daidaito, mutunci, da kuma moriyar juna.
- Cinikin Waje Na Sin Ya Karu Da Kashi 1.3 A Rubu’in Farkon Bana
- Sojoji Sun Ceto Fasinjoji 16 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Filato
Dangane da tattaunawar da bangarorin Sin da kungiyar EU suka yi kan karin haraji da Amurka ta yi, Lin Jian ya ce, bangaren Sin na fatan karfafa tattaunawa da raba dammamakin ci gaba tare da al’umommin kasa da kasa kamar kungiyar EU, ba wai don kawai ya kiyaye moriyarsu ba, har ma ya kare ka’idojin cinikayya da adalcin kasa da kasa.
Game da batun cewa ministan tsaron Amurka da sauran manyan jami’ai sun wallafa maganganun dake yada ra’ayin wai “Sin ta kawo barazana”, Lin Jian ya ce, wasu maganganun jami’an bangaren Amurka suna cike da bambancin akida da tunanin yakin cacar baka, gaba daya karya ce.(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp