Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta bukaci wata jami’ar ofishin jakadancin Canada mai lura da harkokin ‘yan Canada a Shanghai Jennifer Lynn Lalonde, da ta fice daga kasar kafin ranar 13 ga watan nan na Mayu.
Mai magana da yawun ma’aikatar ya ce hakan ya biyo bayan matakin da gwamnatin Canada ta dauka, na dakatar da ikon gudanar da ayyuka ga jami’in ofishin jakadancin Sin mai lura da harkokin Sinawa a birnin Toronto na kasar Canada. Kaza lika Sin ta bayyana matukar adawar ta tare da gabatar da korafi, da rashin amincewa ga gwamnatin Canada.
Jami’in na Sin ya ce matakin na kasar sa martani ne ga mummunan matakin da Canada ta aiwatar, kuma Sin na iya daukar karin matakan ramuwa. (Saminu Alhassan)