Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa na kira ga Japan da ta yi la’akari da kimiyya, da kaucewa aukuwar hadari, tare da yin komai a bude, a manufarta ta zubar da ruwan dagwalon nukiliya.
Wang ya ce Sin na fatan Japan za ta yi matukar la’akari da damuwar sassan kasa da kasa, da al’ummar ta a cikin gida. Ya ce “Na lura da wasu rahotannin kafafen watsa labarai dake cewa, Japan ta shawo kan hukumar lura da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ko IAEA, game da rahoton karshe na hukumar, wanda ke da nasaba da tsarin zubar da ruwan dagwalon na kasar Japan, lamarin da ya kara damuwar kasashen duniya game da manufar Japan din na zubar da ruwan dagwalon cikin teku”.
Wang ya jaddada matsayin kasar Sin, cewa ya wajaba IAEA ta gabatar da rahoton nazarin na ta, bisa goyon bayan kimiyya da tarihi, maimakon amincewa da matsayar Japan na zubar da wannan dagwalo a teku.
Wang ya ce alhaki ne a wuyan Japan, ta yi bayani mai gamsarwa kan wannan yanayi da ake ciki. (Saminu Alhassan)