Yayin taron manema labarai na Larabar nan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya ce kasar sa na fatan sassan kasar Gabon za su shawo kan sabanin dake tsakanin su ta hanyar tattaunawa.
Wang ya ce Sin na fatan sassan za su gaggauta dawo da doka da oda, tare da tabbatar da tsaron lafiyar shugaban kasar Ali Bongo Ondimba.
Kafin hakan dai dakarun sojin kasar ta Gabon, sun ayyana soke zaben kasar da ya gabata, sun kuma ce sun rushe dukkanin sassan gwamnatin kasar, kana sun karbe mulki, tare da tsare shugaba Ali Bongo a gida. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp