Da safiyar yau Juma’a ne ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya gudanar da jerin tarukan manema labarai bisa taken “Ingantaccen ci gaban da Sin ta samu a fannin raya tattalin arziki”, inda jami’ai masu ruwa da tsaki na kwamitin gudanar da kwaskwarima na kasar Sin ya nuna cewa, a shekarar 2024 da ta gabata, Sin ta cimma burikanta na raya tattalin arziki da al’ummarta cikin nasara, matakin da ya aza ingantaccen tubali ga zamanintar da al’ummar Sinawa bisa salo irin kasar Sin.
An ce, mabambantan yankunan kasar na samun bunkasuwa mai dorewa, ana kuma habaka ci gaban aikin kawar da talauci, da gaggauta karkata hanyar da ake bi ta raya tattalin arziki, tare da kiyaye muhalli. Kazalika, da kara bude kofa ga ketare. Baya ga hakan, Sin ta zurfafa hadin gwiwarta da kasashen duniya, da ma kara ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama’a.
A sa’i daya kuma, a shekarar 2024, Sin ta ci gaba da bayyana karfinta na kirkire-kirkire, inda ta kara azama wajen raya sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, matakin da ya sa matsayinta a duniya a bangaren kirkire-kirkire ya daga zuwa na 11 a duniya. (Amina Xu)